Wani dan tiktok yayiwa Rarara martani mai zafi akan wakar arewa na godiya
Wani dan tiktok yayiwa Rarara martani mai zafi akan wakar arewa na godiya
Wani dan Tiktok fitaccen mai amfani da kamar tiktok yayiwa Dauda kahutu Rarara raddi mai zafi akan wakarsa ta “Arewa na Godiya” ya fitar da wakar ne shekaranjiya akan irin nade nade da ankayi na ministoci kuma mawakin yana fadin arewa na dariya wato babu wani hali da arewa take ciki.
Fitaccen mai amfani da kafar tikik sharfaddeen Bature yayi masa martani akan wakar ga abinda yake cewa.
“Shi mawakin yace arewa duk kace arewa kana magana akan jahohi goma sha tara 19 da suke arewacin nigeriya idan kace daukaci kana magana ne akan mutane irin muda muke cikin yankin sune suke godiya kan wannan nade nade da apc na ministoci bayan shi mutane suna godiya suna yabawa bisa ga wannan gwamnati.abinda nake son fadi irin wadannan abubuwa ba abubuwan wasa bane wallahi duk lamarin da yakai mutane suna mutuwa a cikinsa mutane suna rasa rayukansu mutane suna shiga cikin musiba yanzu abun har an fara comedia da harka yunwa , ana maganar rogo da garin rogo wannan ba abun dariya bane.
“A daidai wannan lokaci kake fitowa kake cewa wai mutane suna godiya bayan kasan irin wnanan message sune suke zuwa kunnuwan wadannan Mutane suna ganin abinda suke yi daidai ne ganin suke abubuwan da suke yana iso ga talaka yana mora, maimakon kune ya kamata ku zauna da su ku, ku kuka talatasu kunka nuna suna da alkhairi zasu zamo alkhairi ga mutane maimakon ku gayamusu irin halin da mutane suke ciki na matsi kuyi wakar ko kuje ku same su a’a wai arewa sune godiya.
Kuna tabbatar musu da cewa aikin su na kyau su cigaba abinda suke wallahi wannan cin amana ne kuma wallahi ba abin wasa bane, in wasu bazasu gayamuku gaskiya ba wallahi tallahi sai mun gayamuku gaskiya.
Amma nidai bana godiya ban sani ba ko kai ko ke kuna godiya da abinda ake yi.”
Ga bidiyon nan ku kalla domin jin cikakken bayyani.