Aurena da G Fresh Alameen ya zama dole tunda mun yi gwajin HIV bani da ita Alpha Charles Borno
Aurena da G Fresh Alameen ya zama dole tunda mun yi gwajin HIV bani da ita Alpha Charles Borno
Aurena da G Fresh Alameen ya zama dole tunda mun yi gwajin HIV bani da ita Alpha Charles Borno.
Idan zaku iya tunawa a kwanakin bayane ake shirin auren jaruman TikTok wato G Fresh da fitacciyar mai saida maganin karfin maza din nan Alpha Charles Borno wanda hakan yajawo cece-kuce sosai a kafafan sada zumunta.
Sai kuma daga baya G Fresh Alameen ya fito yana cewa mutane su tsaya da siyan ankon bikinsa dashi da Alpha Charles Borno inda yake cewa har yanzu ba’a yi musu gwajin HIV ba.
Wai ashe dalilin dayasa ya fito yace haka tsohuwar matarsa wato Sayyada Sadiya Haruna yaji tace ai Alpha tana da HIV ganin Sadiya Haruna tace haka yasa ya fito yace aurensa da Alpha yana tangal-tangal saboda har yanzu ba’a yi musu gwajin HIV ba.
Haka yasa Alpha Charles Borno tayi tattaki daga Kaduna zuwa jihar Kano wajen tsohuwar jaruman Kannywood wato Rashida Mai Sa’a domin tarakata Asibiti dan ayi mata gwajin HIV wanda yanzu haka zaku iya ganin bidiyon.
Bayan fitar wannan bidiyon sai kuma akaga G Fresh Alameen da Alpha Charles Borno yana cewa Alhamdulillah yaji dadi anyi gwaji lafiya wanda shima yanzu zaku iya kallon bidiyon.
Me zaku iya cewa dangane da wannan aure na G Fresh Alameen da Alpha Charles Borno ku ajiye mana ra’ayinku a comment section.