Bani da niyyar komawa gidan tsohon mijina Sani Danja, cewar Mansurah Isah
Bani da niyyar komawa gidan tsohon mijina Sani Danja, cewar Mansurah Isah
Tsohuwar fitacciyar jaruma a masana’atar Kannywood wadda ta taka rawar gani, tsohuwar matar fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’atar Kannywood Mansurah Isah tace sam bata da niyar koma gidan tsohon zumanta.
Ana fira da ita a gidan tarin Dw inda mai gabatarwa yake mata tambaya.
Me kike kewa da sani danja?
Tayi dariya ta nuna cewa mai gabatarwa yana neman magana a wajen ta ne amma a cikin raha.
Ina komawa gidan sani danja ?
“A gaskiya kana tambaya ta da sani danja ance zo mu zauna zo mu saɓane , amma gaskiya bana kewar komai saboda dai-dai ne bazan iya ja da ikon Allah ba. A gaskiya bana shirin kome kuma baya cikin tsarina ba yanzu ba, kuma ba nan gaba ba, amma kuma mutum bai san rufi sa ba”- ji mansurah isah.
Ina tabbatar cewa ƴan fim ba su zaman aure?.
A toh ban san inda sunka samu yan fim basa aure ba, saboda a cikin al’umma da ake biliyoyi mu da ko dubu bamu wuce ba ina anka bar sauran , wannan son kai ne da son rai da son zuciya a cikin al’umma.
Ga bidiyon shirar a kasa domin ku kalla.