Duk dan fim din kannywood da bai da rijista zai fuskanci hukunci – Abba El-Mustapha
Duk dan fim din kannywood da bai da rijista zai fuskanci hukunci – Abba El-Mustapha
Idan zaku iya tuwa Hukumar dai ta bawa yan Kungiyar masana’antar kannywood ta MOPPAN damar aikin yin rijistar ga an masana’antar tun a ranar 6/10/ 2023.
Haka kuma, Hukumar ta bada umarnin hana daukar duk wani film ( shooting) ko Sakin sa ba tare da an tace shi ba wanda a cewar ta saba wannan umarnin ka iya saka mutum ya fuskaci fushin doka tare da yin dana sani.
Abba El-mustapha na bayyana haka ne a yau cikin jawabin sa ga manema labarai tare da jagororin ‘yan masana’antar kannywood wanda suka hada da Kannywood Foundation, Arewa films markers, Guild of Artists da kuma yan Kungiyar MOPPAN.
El-mustapha ya kara jaddada cewa ya zuwa wannan lokaci Hukumar tabawa yan masana’antar kannywood wa’adin sati 3 wato daga yau 10/6/2024 zuwa 1/7/2024 da su zo su yi rijista kafin yan kwamitin su fara aiki.
Kwamitin daza su yi aikin sun hada da wakilan kungiyoyin da aka yi wannan zaman dasu a wannan rana ta 10/6/2024.
Ga duk mai bukatar yin rejister da masana’antar kannywood a yanzu zai iya zuwa Kai tsaye ga Hukumar tace fina-finai dake kan titin Maiduguri Road a Hotoro Kano cikin gidan Talabijin din Abubakar Rimi a bene mai hawa uku.
Domin neman karin bayani ku saurari bidiyon.