Uncategorized
FASAHAR KERE- KERE: Wani Yaro Ya Kera Caterpillar, Tractor da Auto Clicker a jihar Jigawa
FASAHAR KERE- KERE: Wani Yaro Ya Kera Caterpillar, Tractor da Auto Clicker a jihar Jigawa
Wannan yaron sunansa MURTALA TANIMU
ALBASU (Daddy) dake yankin karamar
hukumar Suletankarkar ta jihar Jigawa.
ALLAH ya albarkaci wannan yaro da fasaha da kuma basira ta kera abubuwa daban-daban.
A halin yanzu wannan yaro ya kera
CATERPILLAR da TRACTOR da kuma AUTO CLICKER domin yin amfani da ita wajen yin mining.
Tabbas idan wannan yaro ya sami tallafin
karatu daga gwamnatin jiha ko ta tarayya,
zuwa gaba gwamnati da al’umma za su yi
alfahari da shi.
Muna mnasa fatan alkhairi, muna kuma
addu’ar Allah ya kara masa basira.
Daga karshe, muna kira ga gwamnati
musamman gwamnatin jihar Jigawa da ta
tallafawa wannan yaro ta hanyar daukan
nauyin karatunsa domin nan gaba al’umma
da gwamnati su amfane shi.