An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025.
Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya zata iya tsananta a shekarar 2025, inda aka yi hasashen cewa aƙalla mutum miliyan 33 ne za su iya shiga yunwa a shekarar ta baɗi.
a yanzu sun kai kusan miliyan 223.8.
Duba da rikce-rikicen da ake fama dashi a arewacin Nigeria da tabarbarewar tattalin arziki ya jefa kasar wani yanayi, duba da arewacin kasar shine yankin dake dauke da mafiya manoma da makiyaya dake noma sama da rabi da kwatar abinda illahirin al’ummar kasar ke ci aduk shekara, sannan chanjin yanayi ya taka rawar gani wajen kawo tasgaro ga tattalin arzikin kasar, duba da rashin isasshen ruwan sama da wasu yankuna suka tsinci kansu a arewacin Nigeria a daminar banana.
A rahoton, wanda Cadre Harmonisé ta yi a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya, da haɗin gwiwar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya yi hasashen cewa ƴan ƙasar aƙalla miliyan 33.1 ne za su fuskanci yunwa.
Rahoton ya ta’allaƙa hasashen ne kan yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi da rikce-rikice a wasu yankuna na arewacin ƙasar.
Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin Oktoba zuwa Disamban 2024, kimamin mutum miliyan 25.1 ake hasashen za su yi fama da yunwa, duk da cewa lokaci ne na kakar girbin amfanin gona.