Hukumar Hisbah ta rufe Otel na New Palace dake Katsina
Hukumar Hisbah ta rufe Otel na New Palace dake Katsina
Hukumar Hisbah ta Jihar KatsinaTa Rufe Otel Din New Palace a Garin Katsina
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta bada umarnin rufe Otel din New Palace ba tare da bata lokaci ba sakamakon zargin da ake yi na bata tarbiyyar kananan yara mata.
Sanarwar da ta fito daga Hukumar Hisbah, wacce Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an same otel din da karya dokokin hukumar ta hanyar barin kananan yara mata su kwana a otel din.
Hukumar ta gano yara mata biyu kanana a daki daya yayin wani bincike da ta yi kwanan nan, wanda ya saba wa dokokin hukumar.
Hukumar tace wannan shine karo na biyu da ake samun irin wannan laifi a otel din New Palace, duk da gargadin da aka yi a baya da kuma alkawarin da masu gudanarwar otel din suka yi na hana faruwar hakan a nan gaba.
A yayin wani taro na hadin gwiwa da manajojin otel-otel na jihar Katsina, ciki har da manajan otel din New Palace, an amince cewa babu wani otel da zai karbi kananan yara. Duk wanda ya saba wa wannan yarjejeniya zai fuskanci hukunci mai tsanani, in ji sanarwar.
Hakanan tace saboda rashin bin dokokin hukumar da kuma gazawar otel din na cika ka’idojin da aka gindaya, hukumar ta yanke shawarar rufe otel din New Palace ba tare da bata lokaci ba.
Daga ta ce Hukumar Hisbah ta jihar Katsina tana ci gaba da jajircewa wajen ganin an kawo gyara da sanya da’a da ta dace da addini da al’adun jihar Katsina bisa tsarin doka domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Katsina post.