Uncategorized

Labarin abin tausayi da rashin imanin daya faru a jihar Kano kan wata matar aure

Labarin abin tausayi da rashin imanin daya faru a jihar Kano kan wata karamar yarinya

Wannan Labarin ya faru akan idona, a Asibitin Mallam Aminu Kano, ranar Talata 25/06/2024, da misalin ‘karfe 5:30 na yamma, a farfajiyar ‘dakin masu haihuwa  (Labour Room):

Nurse: “Matar ka ba zata iya haihuwa ba, Likitoci sun ce a fa’damaka sai dai ai mata tiyata (CS)”.

Miji: “Caaab! Wallahi bazan iya biyan ku’din nan ba, sunyi yawa. Ya juya wajen Mahaifiyar ta da ‘yan uwan ta, “taje na sake ta saki uku”.

‘Yan Uwanta: “Innalillahi wa Innaa Ilaihi Raji’oon! To ai dama ka ta’ba yimata saki ‘daya.

Miji: “Eh, taje to wannan har na hudu ne”.

Ya tasa ‘keyar sa yai tafiyar sa. A gaban idon mu ‘yan uwanta suka fashe da kuka.

Allah kai mana tsari da zuri’ar mu da ‘yan iska!.

Majiyar mu ta samu wannan bayani ne daga shafin facebook na Ayaha Mahmoud.

Ga cikekkiyar bidiyon shirar nan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button