Others

Matasa Dama Ta Samu: An Sake Bude Shirin Bayar Da Horo Akan Technology

Matasa Dama Ta Samu: An Sake Bude Shirin Bayar Da Horo Akan Technology

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci fatan kowa yana lafiya.

Shirin 3 Million Technical Talent (3MTT) na Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya ya kuduri aniyar habaka kwarewar fasaha a kasa tare da tallafawa hangen nesa na Shugaba Tinubu na samar da ayyukan dijital miliyan 2 zuwa 2025.

Shirin zai taimaka wajen tabbatar da Najeriya ta zama jagora a fitar da kwararru a duniya.

  • Mataki na farko ya fara a Disamba 2023 tare da hadin gwiwar NITDA, inda aka horar da mutane 30,000 a dukkan jihohi da Abuja. An hada karatun kan layi mai zaman kansa da darussa na fasaha ta zahiri tare da tallafın kungiyoyi fiye da 120.
  • Mataki na biyu zai horar da kwararru 270,000 a rukuni uku na 60,000, 90,000, da 120,000.

Wannan matakin zai hada kai da gwamnatocin jihohi, kungiyoyin cigaba, da cibiyoyin koyo don cimma nasara mai ma’ana.

Ayyukan da za’a koyar sune kamar haka:

  • Cybersecurity
  • Game Development
  • Software Development
  • Al / Machine Learning
  • Animation
  • Data Analysis & Visualization
  • Cloud Computing
  • UI/UX Design
  • Product Management
  • Quality Assurance
  • Data Science
  • DevOps

Domin cikewa ku danna Apply dake kasa.

APPLY NOW

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button