Uncategorized

Shawarar Abubakar Maishadda ga matan dake sha’awar shigowa harkar fim

Shawarar Abubakar Maishadda ga matan dake sha'awar shigowa harkar fim

A cewar fitaccen Furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood din, Abubakar Bashir Maishadda: “Don Allah duk wata yarinya budurwa ko wacce ta taɓa Aure da ta ke da niyya ko son shiga harkar Fim ta yi haƙuri, ta je ta yi karatu ko ta nemi wata harkar daban, idan kuma ta samu miji ta yi aure ya fi mata.”

Game da jarumai mata da ke cikin harkar kuwa, a dai cikin zantawar mu da Furodusa MaiShaddan, ya bayyana cewa: “..Yanzu ma harkar a cike take. Suma jarumai (mata)n duka fata na ke yi Allah Ya kawo musu mazan Aure, su yi, su tafi ɗakunan su.

Don ba abun da ya fi dacewa da mace kamar ɗakin ta. Kuma kullum a cikin ba su shawara na ke kan in su ka samu mazan Aure, su yi domin shine mutuncin su.”

Domin sauraron cikakkiyar hirar mu da MaiShaddan kan wannan matsaya ta shi game da ƴan matan Fim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button