Tarihin ‘Ya sarkin kano mai su a Zainab Ado Bayero da ta bambamta da sauran yan uwanta
Tarihin 'Ya sarkin kano mai su a Zainab Ado Bayero da ta bambamta da sauran yan uwanta
Mutane da dama sun yi mamakin ganin guntun bidiyon da na wallafa a shafi na tsakuren hirar da gidan talbijin na TVC ya yi da Zainab Ado Bayero, wadda ta gabatar da kan ta a matsayin diyar marigayi Sarkin Kano,Allah ya rahamshe shi ameen.
Da yawa sun yi mamakin jin cewa ita diyar Sarkin ce har suna shakka ba domin komai ba sai sabida irin shigar ta wadda ta saba wa al’adar hausawa da Musulunci.
Wani ma cewa ya yi shi bai yarda ‘yar Sarki Ado ba ce, to a gaskiya Zainab Jummai diyar takawa ce ta cikin sa.
Mahaifiyar ta ‘yar kabilar Edo ce daga Jihar Edo, Sarkin Auchi ne kakan ta Uwar ta ce Sarkin Auchi ya ba Sarki Ado riko, wato ya kula masa da ita lokacin da ta je karatu a Jami’ar Bayero, Sarki Ado da ita sun haifi ‘yaya biyu, Zainab da kanen ta.
Zainab Jummai ta yi karatu a Ingila da nan Nijeriya, yanzu mai shirya fim ce irin na tarihi da al’amuran yau da kullum wato documentary, kamar yadda majiyarmu ta samu daga mawallafi Ibrahim sheme.
Jummai ta zabi ta bi al’adar da ba ta Hausawa/Musulunci ba, musamman wajen shigar ta.
Wannan zabin ta ne, kuma ba ka isa ka ce don ta yi shigar da ta saba da ta gidan su ita ba ‘yar gidan ba ce.
Uwa-uba ta ce, ita Musulma ce kuma macen kwarai, sannan ta yi kyakkyawar hulda da mahaifin ta.
Ba shakka, ‘yan gidan ba su jin dadin lamarin ta kwata-kwata, a hirarrakin da ta yi da jaridu a baya ta bayyana cewa, sarakunan Kano da Bichi wato wadanda aka tube kwanan nan sun yi kokarin su hana ta yin fim din da ta shirya game da tarihin mahaifin ta da gudunmawar sa ga kasa.
Dalilin su a cewar ta shi ne sabida ita mace ce kuma uwa-uba ba ta bin al’adar gidan su wajen suturta jiki, ta ce shi ya sa duk wanda ta tunkara domin ya taimaka mata sai ya ki.
A cewar ta, duk da zagon kasa da ake yi mata kan wannan shirin fim, ba ta karaya ba domin mahaifiyar ta da wasu mutane daga kudu sun ba ta karfin gwiwa.
To Zainab dai ‘yar Arewa ce ko mun ki ko mun so, kuma ‘yar gidan Dabo ce Fulani ce.
Ko fuskar ta ka kalla ka san hakan ne saka kananan kaya da barin kai a buɗe ba su soke wannan cancantar ba, ko ka ji wani dan gidan ya fito ya karyata ta ne?.
Abin da wasun mu ba su sani ba shi ne akwai ‘yayan Musulmin Arewa da yawa irin Zainab.
Ni kai na na san su da dan dama wato ‘yayan da wadansu manyan Arewa kai har kananan suka haifa da wasu kabilu ko jinsi misali Turawa ko Larabawa ko Canis ko mabiya wasu addinan, kuma suka bi dabi’ar bangaren mahaifiyar su.
Wani babba din ma sai ya mutu sannan ake ganewa ana zaman makoki a gidan Bahaushe/Bafillace/Banufe/Kanuri, sai a ga Bayarabiya ko wani Inyamiri sun zo a matsayin ‘yayan mamacin.
Sau da yawa sai ka ga an hana su cin gado da ake rabawa kamar yadda Zainab Ado Bayero ta ce an hana ta.
Lokaci ya yi da ya kamata mu rage tsattsauran ra’ayi kan faruwar irin wannan al’amarin, ba laifin ‘yayyan da aka haifa ba ne tunda ba su ne suka haifi kan su ba.
Tilas mu rungume su a matsayin namu domin ta haka ne za mu iya dora su kan hanyar da ta dace su bi, kuma mu rufa wa kan mu asiri.
Kyara da tsana ko sharewa da kora ba su iya sauya lamarin su, Hausawa sun ce hannun ka ba ya rubewa ka yanke ka yar!.