Wata mata ta hallaka Ragon laiyar mijinta da muciya sakamakon cinye mata Kullun kosai
Wata mata ta hallaka Ragon laiyar mijinta da muciya sakamakon cinye mata Kullun kosai
Kiki-kaka: Wata Mata Ta Hallaka Ragon Laiyar Mijinta Da Muciya Sakamakon Cinye Mata Kullun Kosai.
Wasu Rahotanni sun tabbatar da mutuwar
wani rago jim Kadan bayan kaishi asibiti
ranga-ranga rai a hannun Allah sakamakon
shirga masa muciya har sau biyar ta hanyar luguden duka da uwargida tayi masa.
Wani ganau ya shaidawa Jaridar Nigeria
Jounals cewa lamarin ya afku ne saboda ya cinye mata kullun kosai da take sayarwa
gaba daya bayan ta shiga ban daki.
Bugu da kari mijinta ya kalubalanceta na
aladolene ta biyashi ragon laiyar shi daya
shafe tsawon lokuta yana kiwo da nufin a
bana shima zaiyi laiya saboda bai taba yi ba.
Anan take dai haniya yaso ya kaure, sai dai
daga gefe an samu kwamitin sulhu domin
gudanar da zama na gaggawa na ganin
uwargidan ta biya mijinta ragonshi data aika lahira a dalilinta na cewa yacinye mata dan jarin da take tattalawa wato kullunta na kosai.
Lamarin ya farune da safiyar jiya juma’a
(7/6/2024) a sabuwar Anguwa ta (Kogoro
Zone2 Kofar Gayan Zariya Jihar Kaduna.
Daga: Abbas Yakubu Yaura.