Uncategorized
Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar mawaki Rarara
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace mahaifiyar mawaki Rarara
A yanzu muka samu labarin cewa masu garkuwa da mutane sun sace mahaifiyar ficaccan mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara.
Mun samu wannan labarin ne daga shafin instagram na BBC Hausa, in sukayi wallafar kamar haka.
Hukumomi a jihar Katsina da ke arewacin
Najeriya sun tabbatar da sace mahaifiyar sanannen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.
A tattaunawarsa da BBC, Kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Mư’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren
Juma’a a kauyen Kahutu da ke karamar hukumar Danja.
Mu’azu ya ce wadanda suka sace matar sun yi hakan
ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.