Zanga-zanga: Ƙananan yaran da gwamnatin tarayya ke tsare da su sabida sun daga tutar Rasha sun shiga wani hali a gaban kotu
An samu hayaniya a babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Juma’a, bayan da wasu daga cikin yara dan da ake tsare da su bisa zargin su da shiga zanga-zangar #EndBadGovernance sun yanke jiki yayin da suke jiran a gurfanar da su.
Kotun ta tsayar da yau Juma’a domin gurfanar da wadanda ake zargin, mafi yawansu yara kanana.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa a lokacin da shari’ar ta fara, an bukaci yaran da suka yi kama da marasa lafiya kuma masu rashin abinci mai kyau, da su matso gaba domin su saurari laifukan su da za a karanta musu.
Yayin da wasu suka yi cincirindo a cikin akwatin masu laifi, wasu kuma sun tsaya a wajen akwatin saboda rashin gurbin zama.
Sai dai, hudu daga cikinsu sun yi saurin fita daga cikin dakin kotu bayan sun yanke jiki sun fadi.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ya yi saurin tashi kafin a samu nutsuwa a dakin kotun.
Bayan zaman kotun ya ci gaba, lauyoyin masu gabatar da kara sun nemi a cire sunayen yaran hudu da suka fadi ba lafiya daga cikin jerin sunayen wadanda ake tuhuma.
Kotun ta amince da bukatar, sauran kuma aka gurfanar da su.
Ana zargin wadanda ake tuhumar 76, wadanda aka kama a Abuja, Kaduna, Gombe, Jos, Katsina, da kuma Kano, da laifin cin amanar kasa da wasu laifuka.